Kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kama matasan Arewa da suke yi wa yan Kabilar Igbo Barazanar korar su daga yankin – Gwamnonin Arewa

0

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta nisanta Arewa daga wata barazana da Kungiyar Matasan Arewa ta yi, cewa ta bai wa dukkan dan kabilar Igbo mazauna yankin Arewa, da su kwashe kayan su a cikin watanni uku su bar yankin.

Da ya ke jawabi a Maiduguri, Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya bayyana cewa gabadayan gwamnonin yankin su na kan tuntubar juna da tuntubar jami’an tsaro na yankin domin su tabbatar da cewa sun kare rayuka da dukiyoyin kowane dan Najeriya da ke zaune Arewa cin Nijeriya.

Bayan wannan, Gwamnonin sun yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta cafke wadanda su ka yi wannan taron da matasan suka yi barazanar bai wa Igbo wa’adin barin Arewa.

Ya kuma kara da cewa wannan mummunar yekuwa da matasan su ka yi, wadanda ba a san ko su wane ba, ta zo daidai lokacin da wasu su ka rika watsa jita-jitar ana shirya makarkashiyar juyin mulkin a cikin kasar nan. Don haka sai gwamnonin suka ce biri fa ya yi kama da mutum.

“Kada a manta, watannin, an rika shigo da makamai kasar nan kuma an rika kwace makamai a hannun wasu, sannan kuma sai ga wasu manyan bindigogi da aka kame, ga kuma jita-jitar yunkurin juyin mulki.”

To yanzu kuma wasu tsiraru kuma tsageru sun kira kan su kungiya, har su na zartas da hukuncin korar wasu daga Arewa. To mu Najeriya kasa daya ce, dukkanmu al’ummar Najeriya ne.”

“Ba za mu rike hannu mu yi tsaye mu kyale wasu tsageru su haddasa mana mummunar fitina ba,”

A karshe gwamnonin su na kira ga dukkan kabilar Igbo mazauna Arewa, su kwantar da hankalin su, kuma su ci gaba da gudanar da harkokin su.

Share.

game da Author