Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i na Kasa JAMB ta sa ranar daya ga watan Yuli domin sake ba daliban da suka sami matsala a jarabawan da akayi kwanaki su sake zama don rubuta nasu.
Babban jami’in dake hulda da jama’a da harkar watsa labarai na hukumar Fabian Benjamin ne ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.
Fabian ya baiyana cewa hukumar ta shirya wannan jarabawan ne domin daliban da suka yi rajista ba da wuri ba da kuma wadanda suka sami matsaloli bayan sun yi rajistan wanda hakan ya sa ba su rubuta jarabawan a wancan lokacin ba.
“Bayan tattaunawan da hukumar ta yi ne ta amince ta ware ranar Asabar 1 ga watan Yuli domin rubuta jarabawan”
“Dalibai 85,000 ne zasu rubutar jarabawar”
“Mun kuma tura sako ta wayan tarho wa duk wadanda suka cancanci rubuta jarabawar”
“Sakon ya shaida wa daliban cewa su duba e-mail dinsu ko kuma adireshin mu ta yanar gizo domin samun karin bayani akan jarabawar.”
Hukumar ta kuma gargadi daliban da za su rubuta jarabawar da su guji aikata wani abu da zai sa su sami wata matsala lokacin jarabawar.”