Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta gargadi mutane kan illolin zukar Taba Sigari

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya rubuta wata wasikar ta musamman zuwa ga ministan Shari’a Abubakar Malami da Sifeto janar din ‘yan sandan Kasa Ibrahim Idris domin neman goyan bayan su kan shirin da ma’aikatar ta ke yi na kafa dokar hana zukar taba Sigari.

A wasikar Minista Adewale ya ce ‘’Ya zama dole mu hada karfi da karfe domin kafa wannan doka na hana shan taba sigari mai suna NTC Act 2015 domin kare lafiyar mutanen kasar’’

Ministan ya kuma aika da wannan wasikar zuwa ga hukumar NDLEA da kuma shugaban ma’aikatan gwamnati domin neman su mara wa wannan kudiri baya.

A hiran da ya yi da gidan jaridar PREMIUM TIMES Isaac ya yi mana bayanin matakan da ma’aikatar sa ta riga ta dauka kan siyarwa da shan Taba Sigari zuwa yanzu.

Ga Dokokin:

1. An hana siyar da sigar wa duk wanda bai kai shekara 18 da haihuwa ba.

2. An hana siyar da sigari kara-kara sai dai kwali.

3. Za a siyar da sigari wanda baya fitar da hayaki da ya wuce gram 30.

4. An hana talla ko kuma siyar da sigar ta kafofin yanar gizo.

5. An hana kamfanonin sarrafa sigari saka baki akan abubuwan da ya shafi kiwon lafiya.

6. An hana amfani da sigari a duk wuraren da yara ko kuma ake kula da yara da kuma duk inda mutane suke wanda ya hada da tashar mototoci, wuraren shakatawa,wuraren cin abinci da makamantansu.

7. Za a hukunta duk duk wani mamallakin wuraren da aka Ambato da ya bari aka sha sigari a wurin sana’ar sa.

8.An hana yin tallata sigari ta kowace kafa ko hanya ko kuma tallafa wa kamfanoni irin haka.

9. A tabbatar an Kiyaye wannan dokoki.

Share.

game da Author