Gamayyar kungiyoyin tsagerun yankin Neja Delta su 9, sun yi kira ga ‘yan arewacin Najeriya da kuma kamfanonin hakar danyen mai da su bar yankin cikin gaggawa.
Ƙungiyoyin sun ba ‘yan arewa da ke zaune a yankin wa’adin nan da ranar 1 ga watan Oktoba su fice daga yankin ko su kuka da kansu.
Haka kuma, sun bukaci gwamnatin Najeriya ta mayar musu da duk rijiyoyin man da ‘yan arewacin kasar suka mallaka a yankin cikin gaggawa.
Suma kungiyar MASSOB masu fafutukar kafa kasar Biafra suka umarci ‘yan duk wani dan kabilar Igbo da ya tattara komatsensa ya dawo gida daga yankin Arewa.
Kamar yadda gidan Jaridar BBC Hausa ta ruwaito wannan labari, Shugaban Kungiyar MASSOB Uchenna Madu ya ce sun kammala shiri tsaf domin yi wa ‘yan kabilar Igbo din lale marhaba. Sannan ya ce sunyi hakane gudun kada a shammace mutanensu kamar yadda akayi musu a 1966-67.
Da BBC ta ankarar da Madu irin Alkawurran da Sarakuna da gwamnonin Arewa su ka yi wa ‘yan Kabilar Igbo din mazauna yanki, yace wannan maganar kanzon kurege ne domin bakin matasan daya da shugabanninsu.