Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa NPHCDA Faisal Shuaib ya ce kusan kullum mata da yara kanana 3,000 ne ke mutuwa a dalilin cututtukan da za a iya kawar da su a kasa Najeriya.
Ya ce yara kafin su kai shekaru biyar suke mutuwa a ta dalilin haka.
Ya fadi hakan ne a taron da aka yi akan hada kan cibiyoyin kiwon lafiya domin samar da ingantacciyar kiwon lafiya da aka yi a Abuja inda ya ce ‘’Samar da ingantacciyar kiwon lafiya ce kawai zai iya kawar da matsalolin dake tattare da irin wannan cututtukan da fannin kiwon lafiya ke fama da su.”
‘’Mutuwan mata da yara kanana 3,000 ya nuna cewa kowace jihar na rasa mata da yara kanana da yawa a kowace wata sanna kuma kusan kullum ana samun mutuwar mata da yara 80 daga cututtukan da za a iya kawar da su”.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kara kudaden da take ware wa ma’aikatar Kiwon Lafiya sannan kuma dole ne kungiyoyi masu zaman kansu su ci gaba da samarwa fannin tallafi domin samun nasara akan kawar da iri cututtukan da za a iya kawar wa mai makakon bari yana kashe yara kanana.
Discussion about this post