Ranar Juma’a ne a Abuja kasar Amurka da Najeriya su ka kulla yarjejeniyar naira bilyan 147.5 domin tallafawa kan shirin hana kamuwa da yaduwar cutar kanjamau.
An dai kulla yarjejeniyar shirin mai suna COP ne, a tsakanin Jakadan kungiyar U.S Global AIDS, Deborah Brix da kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Hana Yaduwar Kanjamau na Najeriya, NACA, mai suna Sani Aliyu.
Cikin wadanda suka halarci bikin kulla yarjejeniyar har da Jakadan Amurka da ke Najeriya, Stuart Symington, wanda ya ce Nijeriya da ofishin jakadancin Amurka su na aiki kafada-da-kafada domin kawo kyakkyawan sauyi a Nijeriya.
Birex ta kara da cewa COP shiri ne na shekara-shekara tsakanin gwamnatin Amurka da kuma Nijeriya a kan hana yakuwa da kamuwar cutar kanjamau.
Shiri ne kuma a cewar ta na, musamman da ke fitowa kai tsaye daga ofishin Shugaban Amurka domin kokarin da kasar ke yi wajen dakilewa da kuma hana kamuwa da cutar.
“Daga lokacin da aka kirkiro shirin cikin 2004 zuwa yau, shirin PEPFAR ya kashe dala bilyan 4.3 wajen tallafa wa hana kamuwa da yaduwar cutar kanjamau a Nijeriya.” Inji Jakadar.
Jakadar ta ci gaba da cewa gwamnatin Amurka mai ci yanzu, ta kudiri aniyar tallafa wa Najeriya ne ganin yadda gwamnatin Najeriya mai ci a yanzu ita ma ta dauki shirin hana yaduwa da kamuwar cutar kanjamau da muhimmancin gaske.
Ta ci gaba da cewa wannan tsari abu ne mai matukar tasiri, kasancewa zai bada hasken yadda za a hana yaduwar cutar kwata-kwata nan da shekarar 2020.