Dalilin da ya sa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya -Ministar Kudi

0

Ministar Kudi Kemi Adeosun, ta bayyana cewa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya saboda kudin gwamnati ba su da wahalar sacewa.

Da ta ke jawabi a wurin wani taro da Kwamitin Sa-ido kan hana cin hanci da rashawa, wanda ke karkashin ofishin Shugaban Kasa ya shirya a ranar Talata, ta ce gwamnatin tarayya na bakin kokarin ta wajen kara zakulo dabarun hana wawura da harkallar kudi a kasar nan.

Taron dai na hadin guiwa ne har da Ma’aikatar Shari’a ta kasa. Kemi ta kara da cewa, haka kuma gwamnati na daukar wasu matakan na yadda ajiyar kudin sata a kasashen waje zai zama da matukar wahala ga wanda ma ya saci kudin daga nan Najeriya.

Wata hanyar dakile yawaitar satar kudin kuma ita ce wajen kara kaimin bin dokoki da ka’idojin da hajari suka tanada. Hakan ta ce ba karamin tasiri zai kawo wajen hana wawurar dukiyar kasar nan ba.

“Darasin da nan koya a yanzu zama na Ministar Kudi ya nuna min, kuma ya sa ina da yakinin cewa wadannan matakai za su iya yiwuwa a nan Nijeriya. Don haka tilas ne mu tashi tsaye mu dauke su.”

“A matsayin abin da na fahimta a zama na Ministar Kudi, kwato dukiyar da aka wawura abu ne mai kara min kaimi kuma ya na kara zaburar da ni. Sai dai kawai a ce abin zai dauki shekaru. Kun san kuma an ce daukar matakin hana aukuwar barna ya fi alfanu, a bisa neman maganin warkar da barna bayan ta auku.” Inji Minista Kemi.

Share.

game da Author