Muna nan a kan bakarmu na kowani dan Kabilar Igbo ya koma ‘yankinsa – AYCF

1

Kungiyar matasan Arewa ‘Arewa Youth Consultative Forum, AYCF ta ce duk da cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi barazanar kama su da kai su kotu suna nan a kan bakan su na dole fa duk wani dan kabilar Igbo ya bar yankin Arewa nan da watanni uku masu zuwa.

Kungiyar ta ce ko wani Inyamiri ya koma garnish kawai.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar AbdulAziz Suleiman ya ce babu gudu ba ja da baya akan abin da suka shirya kuma suka sa a gaba.

Da yake hira da gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta wayar tarho, Suleiman yace “ Ba kira muke yi da ayi tashin hankali ba. Dama can ‘yan kabilar Igbo sun ce ba ruwan su da Najeriya saboda haka su tafi abinsu kawai shine muke kira suyi.

Game da barazanar kama su da gwamnan Kaduna yayi ikirarin yi, Suleiman yace El-Rufai na yin haka ne saboda son zuciya da siyasa.

“ Menene El-Rufai yayi lokacin da Inyamirai suka kori fulani daga yankin su. Me yayi akai.

“ Ina yake da aka kashe ‘yan Arewa sama da 500 a Ile Ife. Saboda yana so ya yi takaran shugaban kasa ne shine yasa yake nuna ko oho ga mutanensa ya na manne wa ‘yan kabilar Igbo din. Ya je Allah ya bashi sa’a.

Kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, MASSOB ta yi kira ga ‘yan Kabilar Igbo da ke zaune a Arewacin Najeriya da su fara shirin dawowa gida.

Shugaban kungiyar Uche Madu ya ce kowani dan Kabilar Igbo ya tattara kayansa da dawo su gina yankinsu na Biafra.

Share.

game da Author