Garba Shehu ya karyata rade-radin da ake ta yadawa game da dalilan da yasa aka ci gaba da ajiye jirgen da ke daukar shugaban kasa a kasa Ingila.
Ya ce kamar yadda dokar rundunar Sojin Saman Najeriya yake, ba zai yiwu ace jirgin baya kusa da shugaban kasa a ko ina yake ko dan tsaro.
Buhari bashine farau ba.
“ Duk shugabannin kasar da suka gabata sun yi irin haka, wasu ma sukan yi tafi ne da jirage har uku amma hakan bai zamo abin cece-kuce ba.
“ Abin da zance anan shine inyi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa irin wadannan maganganu kunne uwarshegu domin wannan gwamnati ta sa ayyukan samar da ababen more rayuwa ne ga mutane.
Daga karshe Garba Shehu ya ce gwamnati na ci gaba da gina gadan Nija da ke yankin kudu maso gabas, da sabuwar tashan wutan lantarki dake Mambila da titunan jiragen kasa da zai hada Kudu da Arewa.