Ministan Tsaro Janar Mansur Dan’ali mai ritaya, ya bayyana cewa Najeirya na kokarin ganin ta shawo kan rikicin makiyaya da manoma da kuma matsalar yawaitar satar shanu da ake fama da su, musamman a Arewacin kasar nan.
Dan’ali ya yi wannan bayani ne a wurin taron da ministoci suka shirya, wanda aka kammala yau a Abuja, domin amsa tambayoyi da kuma jin ra’ayin jama’a. Ya ce, sun gano cewa fantsamar muggan makamai a Afrika ta Yamma tun bayan rikicin kasar Libya, ta haifar da yawaitar safarar makamai a Afrika ta yamma, har abin ya yi mummunan tasiri a Arewacin Najeriya.
Kan haka ne ya ce tuni sun kamo hanyar dakile wannan fantsamar makamai ta hanyar yunkuri na hadin guiwa da wasu kasashe ke yi ciki har da Najeriya, Nijar da Mali, domin a tsananta tare duk wasu hanyoyi da ake safarar makamai daga wannan kasa zuwa waccan a Afrika ta Yamma.