Kamfanin GAVI ta samar da Allurar rigakafin cutar Ebola wa kasar Kongo

0

Kamfanin sarrafa magani wanda ake kira da ‘Gavi global vaccine alliance’ ta sanar da cewa ‘Merck’ ta samar da isassun alluran rigakafin cutar Ebola.

Sanarwan ta fito ne bayan kungiyar kiwon lafiyar ta duniya WHO ta sanar da bullowar cutar a Kongo.

Aluran rigakafin mai suna ‘rVSV-ZEBOV’ ya samu ne bayan gwajin ingancinsa da aka yi a shekaran 2016.

Kakakin kungiyar ‘WHO’ ya fada wa manema labarai cewa a ranar Juma’a ne suka sami labarin bullowar cutar Ebola a kasar Kongo kuma har mutum daya ya rasa ransa.

Yace ita wannan rigakafin ana iya bada da ita ce kamar yadda ake bada rigakafin cutar gaida.

Ya ce ma’aikatan kiwon lafiyan suna bi gida-gida ne domin yi wa mutanen da sukayi cudedeniya da wanda ya kamu da cutar da makwabtansa domin dakile yaduwar cutar.

Ya ce a shekaran da ta gabata ne suka sami tabbacin ingancin maganin bayan su sun gwada maganin a shekaran 2015 akan mutane 11,841 wanda suka kamu da cutar sannan kuma daga cikin su mutane 5,837 sun sami saukin cutar a wancan lokaci.

Ya kuma ce sun yi wannan gwaji ne tare da ma’aikatan kiwon lafiyar kasar Guinea, Medecins Sans Frontieres, wata asibitin kasar Norway da kuma wasu kungiyoyi.

Share.

game da Author