Rundunan ‘yan sandan jihar Nasasawa ta gargadi iyaye a jihar da suyi kaffa-kaffa da shige da ficen ‘ya’yansu musamman ganin yadda ake ta hasarar yara ta hanyar yankan kansu da akeyi.
Rundunar ta sanar da haka ne bayan tsinto ganganjikin wani yaro dan shekara 5 da kayi a jikin wani kangon gini da aka jefar bayan an yanke kan sa.
Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Kennedy Idirisu ya ce an tsinto gangan jikin yaron ne a wani kangon gini a ranar Litini da misalin karfe tara na safe.
Ya ce sun fara gudanar da bincike akan mutuwar yaron sannan kuma ya kira ga iyaye da su sa ido akan shige da ficen ‘ya’yansu a ko da yaushe.
Innan yaron Mary Adogo ta ce Meshach ya fita zuwa bandaki ne a daren Lahadi inda daga nan ba a sake ganinsa ba.
Mary ta ce ta mahaifiyarsa da ta ga bai dawo ba sai ta nemi ‘yan uwa da makwabta su a taya ta neman sa.
Ta ce a haka ne fa kawai sai aka tsinto gangan jikinsa ba tare da kai ba a jikin wata kangon gini da ke kusa da gidan su.
Ta ce sun iya gane gawan yaron ne saboda rigar da ya ke sanye a jikinsa.