Akwai sauran laifukan da Dasuki bai wanke kansa akai ba shi yasa yake daure haryanzu – Gwamnatin Najeriya

0

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya ce gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da daure tsohon mai ba shugaban Kasa shawara akan harkar tsaro Sambo Dasuki saboda duk da cewa Kotu ta bada belinsa ba a sake shi bane saboda akwai wasu laifuka da ake tuhumarsa da shi ko alkalansa basu warware su ba.

Yace dalilin haka ne yasa gwamnati za ta ci gaba da daure shi har sai an kamala dukkan binciken da akeyi akansa.

Garba Shehu ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a hira da akayi dashi kan nasarorin da mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu shekaru biyu bayan an rantsar da ita.

“Akwai sauran laifuka da ake neman ya wanke kansa akansu kuma har yanzu baiyi hakan ba gami da bincike da gwamnati take yi akan su duka da ba a gama ba. Hakan yasa ba zai yiwu a sake shi ba sai an gama wadannan bincike.”

Share.

game da Author