Kafin a kai ga bayani na musamman a kan hayakin da ya tirnike Kano da Arewacin kasar nan, dangane da yinkurin binciken Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, duk da dai gwamnatin jihar Kano ta janye batun rikicin, Mun yi nazari domin tabo cikakken bayanin rashin jituwar nan.
Sai dai kuma ya na da kyau kafin nan, mai karatu ya san ya karfi, tasiri da martabar masarautar Kano ya ke a da, da kuma yanzu? Ya martaba da bambancin Sarakunan Kano ya ke? Me ya bambanta kowane Sarkin Kano da sauran sarakunan zamanin sa?
Ba za a fahimci guguwar batun binciken Sarki Muhammadu Sanusi na II ba, sai an fahimci rayuwa, siyasa, mulki, karfin iko da kuma guguwar da ta yi sanadiyyar tube kakan sa Sarki Muhammadu Sanusi I. Daga nan, sai kuma a gangaro a gane shin su wa ne ne magautan Sarki Muhammadu Sanusi II, na sarari da na boye?
Ko me ya sa gwamnatin Jihar Kano ta fasa binciken? Za a ji komai idan aka biyo mu dalla-dalla.
An hafi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, wato kakan wannan Sarki na yanzu, a cikin shekarar 1905, shekara biyu bayan Turawan Muilkin Mallaka sun ci Kano da yaki. Shi ne Sarki na 11 a jerin Sarakunan Daular Fulani, sannan kuma Sarki na 54 a jerin Sarakunan Kano baki daya.
Tarihi ya tabbatar da cewa Sarki Muhammadu Sanusi 1 ya kasance mai ilmin addinin musulunci da kuma ilmin zamani. Ya riki sarautar Ciroman Kano, wato Hakimin Bichi, kuma ya kasance an ba shi nauyin kula da sauran yankunan hakimai. Wannan ya ba shi karfin fada-a-ji sosai a sha’anin tafiyar da mulkin masarautar gargajiya a yankin mulkin Kano, wadda a lokacin ta nausa gabas har zuwa Azare.
Ko a zamanin ya na Hakimin Bichi, bincike ya gabbatar da cewa dagatan da ke kaskashin Bichi ba su kasa ga 90 ba. Sarki Sanusi ya taba zama wakili a majalisar wakilai ta Yankin Arewa a cikin 1947. Kuma ya zama Minista Maras Ofis cikin 1952, kamar yadda Paden ya fada a cikin littafin sa.
Muhammadu Sanusi ya zama Sarkin Kano cikin watan Disamba, 1953. Ya kasance a lokacin da ya hau sarautar Kano ya na da kwarewa sosai a sha’anin mulki, saboda mahaifin sa Sarki Abdullahi Bayero ya wakilta masa tafiyar da sha’anin mulki a karkashin Turawan Mulkin Mallaka a lokacin.
Sarki Sanusi 1 cikakken dan siyasa ne, ya na daya daga cikin kusoshin da su ka kafa jam’iyyar NPC. Sannan kuma ya taimaka kwarai wajen shigo da ‘yan kasuwa ko ‘yan tireda da masu ilmi a cikin jam’iyyar, musamman abokan sa masu ilmi. An ce ya taimaka wa Sardauna a lokacin da ya samu matsala da Sarkin Musulmi Abubakar na Uku. Ya tsaya tsayin daka wajen ganin an zabi Sardauna ya zama shugaban jam’iyyar APC. An ce shi ne ya fi karfi a cikin jam’iyyar wajen ba ta goyon baya sosai.
Ya yi karfi sosai har ta kai babu wani Sarki da ya fi shi ko kai shi kwarjini a lokacin, musamman idan aka yi la’akari da cewa yankin mulkin sa ya fi kowane yawa a Arewacin Nijeriya a lokacin.
Lokacin da Gwamnan Arewa na Mulkin Mallaka, Sir.G.W Bell zai nade kayan sa ya koma Ingala bayan samun ‘yanci, an nada Sarki Sanusi zama Gwamnan Arewa na Riko a shekarar 1961.
Gwargwadon karfin iko da martabar Sarkin Kano Sanusi 1, gwargwadon martabar Kano a idon Turawan mulkin mallaka da Arewa gaba daya. Duk da kasancewa Sarkin Kano shi ne na hudu a jerin martabar Sarakunan Arewa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 1 ya fi kowa yawan albashi a lokacin, har ma da sauran ma’aikatan Arewacin kasar nan. Wani rahoto ma ya nuna cewa Sarkin Kano da ya yi zamani da Gwamna Lugga, ya nunka shi albashi.
Sabani ya shiga tsakanin Sarki Sanusi da babban aminin sa Sardauna, Firimiyan Arewa, har ta kai an zarge shi da salwantar da wasu kudade, wanda hakan ya sa aka kafa masa kwamitin bincike a karkashin wani Bature mai suna D. M. J Muffet a cikin 1962. Daga bisani an ce an same shi da laifi, inda Gwamnan Arewa Sir. Kashim Ibrahim ya kira shi ofis ya shaida masa cewa ga abin da bincike ya same shi da shi. Nan take ya rubuta takardar sauka daga sarauta, kamar yadda aka nemi ya yi,inda aka tambaye shi inda ya fi so ya zauna, shi kuma ya ce ya fi son Azare.

Sai dai kuma bincike da dama sun nuna cewa siyasa ce ta yi sanadiyyar cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I daga mulki, ba salwantar kudi ba. Wadannan dalilai na siyasa su na da yawa. Sai dai kuma a wata tattaunawa ta musamman da na taba yi da Sarkin Musulmi Marigayi Mai Alfarma Ibrahim Dasuki, ya shaida min cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I mutum ne kaifi daya, wanda bai yarda da raini ba, kuma bai yarda a taka shi ba, ko kai wane ne.
A cikin wannan tattaunawa Ibrahim Dasuki ya ba ni wani labarin yadda aka watse baram-baram tsakanin Sarkin Musulmi Abubakar III da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I:
“Mutum ne wanda ba ya son raini, kuma mai tsare gida, mai ji da kan sa. A lokacin da, idan Sarakunan Musulunci suka sayi wasu kaya masu alfarma da tsada daga hannun fatake, sai su ce ku je Kano a biya ku. Wato ku je Sarkin Kano ya biya ku. To wata rana wasu Buzaye su ka kawo wa Sarkin Musulmi Abubakar wasu kayan ciniki. Yaban ya saya, sai ya ce masu su je Kano a biya su.”
Sultan Dasuki ya ci gaba da shaida min cewa, “Su dai fataken nan sun saba idan sun je Sokoto, kai tsaye su ke ganin Sarkin Musulmi. Amma da suka je Kano, sai da suka yi kwana biyu kafin su ga Sarki. Sannan kuma bayan ya ji abin da ke tafe da su, ya ce a fada musu su koma Sokoto a biya su, shi ba zai biya ba.” Cewar Sultan Dasuki.
Dangane da binciken sa kuwa, PREMIUM TIMES Hausa ta ci karo da wani bayani a cikin wata kafar tattara bayanai na masarautar Kano ta intanet da ke nuni da cewa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I bai salwantar da kudin da aka zarge shi ba, amma dai ya ciri fam dubu shida ne a matsayin ramce ga yankin mulkin Kano, inda aka yi amfani da kudin wajen gina masana’antun farko a Kano da ke Bompai.
An ce dama kuma manyan ministocin Yankin Arewa da ke Kaduna sun fara dora masa karan-tsana. Ganin haka ne aka kulla masa tuggun daina tura kudi a maitulmalin Kano, domin matsalar rashin kudi ta faru, tunda ya rigaya ka karbi ramce a lokacin. An ce duk da ya nuna takardun shaidar abin da ya yi da kudin. Hakan bai hana a ce bai yi laifi ba.
Cire Sarki Sanusi I ya haifar da hayaniya a Arewa. Na farko dai Kanawa sun rika kallon cewa an ci mutuncin su. Don haka nan da nan manyan ‘yan siyasa suka yi taron gaggawa, inda nan take suka jam’iyyar Kano Progressive Party, KPP, a ranar 16 Ga Afrilu, 1963, wadda a cikin watanni kadan ta samu rajistar mambobi har dubu 36,423. Sannan kuma ta nemi kawance da sauran jam’iyyu irin su NEPU ta Malam Aminu Kano, UMBC ta Middle Belt, wato Arewa ta Tsakiya. Da kuma wata jam’iyyar ‘yan ra’ayin rikau ta Zamfara, wadda ta yi zazafar adawa da NPC ta su Sardauna.
Wannan kawance ya kara karfi, domin dimbin mabiya Darikar Tijjaniyya sun rika tururuwa a cikin jam’iyya a garuruwa daban-daban, kasancewa Sarkin Kano Sanusi ya zama Halifan Shekh Ibrahim Nyass a Nijeriya.
Jam’iyyar KPP ba ta yi tasiri sosai ba, domin Murabus Sanusi bai yarda ya jingina ko ya jibinta da ita ba, kuma ba ta da karfin rike dawainiyar kan ta kamar NPC jam’iyyar gwamnai. Sannan kuma, an rika bin wasu jigajigan ta ana kamawa ana kullewa a matsayin adawa.
Sarkin Kano Muhammdu Sanusi II
Ba tun yau ko jiya ya saba da kushe, caccaka ko bakaken maganganu ba. Tun ma kafin ya zama gwamnan babban bankin tarayya, CBN, ya saba fadar albarkacin bakin sa a kan duk wani al’amari da ya shafi kasar nan ko jihar Kano. Duk wasu rikice-rikice na baya har zuwa cirewar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya yi masa daga shugabancin bankin CBN, bayan ya fallasa cewa Dala Biliyan 20 ta salwanta, duk sun zama tarihi.
Sabuwar magana a yau ita ce zargin da gwamnatin Kano ta yi masa, wanda shi ma a ranar Litinin da ta gabata, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rubuta wa majalisar Kano wasikar neman su janye binciken, kuma suka janye.
Sauran maganganun da ke baya su ne, shin su wane ne ke neman ganin an cire Sarkin Kano, idan har akwai masu bukatar haka din? Me ya sa Ganduje ya yanke shawarar a janye binciken? Shin maganganun da Sarkin ya fada sun kai a tayar da jijiyar wuya har a nemi kafa masa kwamitin binciken da a karshe za a yi masa bi-ta-da-kullin-tubewa?
Ko tantama babu ra’ayoyin jama’a da wasu majiyoyi da dama sun nuna akwai wadanda suka rika rura wutar fitinar binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Lokacin da aka nada shi Sarkin Kano a shekarar 2014, dan majalisar jihar Kano mai wakiltar Birni da Kewaye a yanzu, Honarabul Babba Babba Dan’Agundi na daya daga cikin zaratan da suka tsaya tsayin daka suka bude hanya, bayan an fasa bangon gidan Sarki, aka yi wa Sabon Sarki hanyar shiga cikin gidan sarautar Kano. Baffa ya tsaya tsayin-daka bayan an samu tirjiya daga wasu gungun masu adawa da nadin sabon sarkin.
Jama’a da dama sun yi mamakin yadda a lokaci guda Baffa ya tubure a majalisa, ya goyi bayan a binciki Sarki, kuma aka nada shi mataimakain shugaban kwamitin bincike. Sai dai kuma jama’a da dama sun yi ittifakin cewa adawar sa ba ta rasa nasaba da haushin da su ke ji ganin yadda Sarki bai maida wa yayan Baffa din sarautar sa ta Hakimin Gabasawa ba, kuma Sarkin Dawaki Mai Tuta.
Marigayi Sarki Ado Bayero ne ya cire Aminu Babba Dan’Agundi daga sarauta, inda shi kuma ya garzaya kotu ya shigar da kara, aka yi ta shari’a.
Alamomi da yawa sun nuna cewa a baya akwai kyakkyawar alaka tsakanin Aminu Babba da kuma Sarkin Kano a lokacin da ya ke Gwamnan Babban Bankin Tarayya, CBN, har zuwa hawan sa karagar sarautar Kano.
Majiyoyi da yawa na yada cewa an yi tsammanin Sarki Muhammadu Sanusi II zai maida wa Aminu rawanin sa. Ganin ba a maida masaba, ya sa da dama ke tunanin hakan na da nasaba da yadda Baffa kanin Aminu din ya zakalkale a kan batun sai an binciken Sarki. Har yanzu shi ma Aminu babu wata sarauta a kan sa.
Shi kan sa shugaban jam’iyyar APC bangaren gwamnati na jihar Kano, Abdullahi Abbas, akwai da dama masu zargin hannun sa a wurin rura fitinar binciken Sarki. Abdullahi Abbas dai da ne ga Galadima Kano Abbas Sanusi. Shi kuma Abbas Sanusi, kanin Lamido Sanusi ne, mahaifin Sarkin yanzu, Muhammadu Sanusi II. Wasu na yi wa Abdullahi Abbas kallon a matsayin sa na jikan Sarki Muhammadu Sanusi I, akwai bukata da kwadayin sarautar a zuciyar sa. Don haka ko da sarauta ta fadi, Abdullahi Abbas zai iya nema. Idan ya samu kuwa ba za a yi mamaki ba, domin ya gada.
A wani gefen kuma, akwai masu zargin wasu da suka yi takarar sarautar tare da Sarkin na yanzu, amma ba su samu ba. Duk da dai ba a fito an bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA sunayen su ba, idan ba a manta ba, Sanusi Ciroma, daya daga cikin wanda ya nuna son sarautar, har wasu suka rika yada rudu da ji-ta-ji-tar cewa shi aka nada, ya kasance a yanzu babu wata sarauta a hannun sa.
Kafin nan kuwa shi ne Ciroman Kano. Sarki Muhammadu Sanusi II shi ya tube rawanin sa, ya nada wa kanin sa Nasiru Ado Bayero a matsayin Sabon Ciroman Kano. Da yawan mutane a Kano su na cewa har yau bai huce ba.
An kuma yi zargin akwai wani daga cikin maneman sarautar da ya bi wasu manya a kasar nan ya damfara musu milyoyin kudade a daidai lokacin da guguwar binciken ta tirnike.
Har ila yau, an rika jefa zargi a kan gwamnan Zamfara, Abubakar Yari, wanda aka ce bai ji dadin yadda Sarkin ya fito a bainar jama’a ya caccake shi ba dangane da kasassabar da gwamnan ya yi, inda ya ce annobar sankarau da ta addabi jama’a musamman a jihar sa, Zamfara, ta na da nasaba da aikata alfasha da jama’a ke yi, Allah ke fushi da su, ya aiko musu da cutar sankarau.
A matsayin Gwamna Yari na shugaban kungiyar gwamnoni, wasu sun rika zargin cewa ya na da karfin tunzura Ganduje a nemi binciken Sarki, domin su huce-haushi.
Ko shakka babu, Gwamna Umar Ganduje shi da ‘yan majalisar jiha sun ji haushin yadda Sarkin Kano ya kalubalanci shirin ciwo bashin bilyoyin nairori masu tarin yawan da suka shige tunanin mai tunani, wadanda ba a san ranar biya ba, domin a yi titin jirgin kasa. Wannan shiri dai Sarki ya ce ba shi da wata fa’ida ga ci gaban jihar Kano.
Akwai kuma masu ganin cewa Sarki ya maida kan sa kamar wanda ya fi kowa sanin matsalolin da suka shafi al’umma, dubi da wasu shirye-shiryen gyaran dabi’un al’umma da ya dauko aniyar yi. Don haka maimakon ya rika bai wa gwamnati shawara a asirce, sai ya koma ya na gwasale jami’an ta har da gwamna a bainar jama’a.
Ganin yadda Ganduje ya nemi ‘yan majalisar Kano su janye binciken kuma su ka amince, jama’a da dama na masu ra’ayin cewa baya ga dalilai na sa bakin da gwamnan ya ce wasu manya sun yi ne suka sa ya nemi a janye bincken, ana ganin akwai kuma dalilai na matsalar siyasa da wasu su ka hango wa gwamnan wadanda ka iya zame masa alakakai a nan gaba.
An yi mamakin yadda Ganduje ya dauki batun Sarkin Kano da zafi, har batun binciken sa ya taso, a daidai lokacin da wasu ke ganin gaskiya ce Sarki ya fada. Masu sharhin siyasa na ganin binciken Sarkin Kano, ko yanke wani hukunci a kan sa, zai iya shafar yinkurin tazarcen Ganduje, bisa la’akari da cewa masu adawa da shi sun karu, ga shi kuma ba ya ga-maciji da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ubangidan sa, kuma wanda ya yi wa mataimaki har tsawon shekaru takwas.
Wasu kuma na masu ra’ayin cewa fushi da Sarki ko cire shi, zai iya shafar jam’iyyar APC kan ta a Kano, domin dama akwai abin da Hausawa ke cewa iska-ya-tadda-kaba-na-rawa. Da farko dai APC ta dare gida biyu a Kano, wato Kwankwasiyya da Gandujiyya. Kara tulin makiya a bangaren Ganduje, kamar burma wa cikin sa wuka ne a siyasance, yadda abin zai iya shafar Kano baki daya.
Ba mamaki Ganduje ya hango gagarimar matsalar da aka ce an nuna masa, shi ya sa ya nemi a daina binciken Sarki, kuma a ranar da aka bayyana daina binciken, a karon farko ya fito ya na yabo da jinjina ga Kwankwaso, a matsayin wanda ya kira gwarzon sa wajen jerin mashahuran gwamnonin farar hula da suka yi wa Kano aiki, tun bayan gwamna marigayi Abubakar Rimi.
Yanzu dai daga Sarki har Gwamna, za a iya cewa kowa ciki lafiya, baka lafiya. Idan ma ta-ciki-na-ciki, to sanin gaibu sai Allah.
Sai dai akwai wata sabuwa, inji ‘yan caca, daidai lokacin da PREMIUM TIMES HAUSA ke rubuta wannan nazari, labari ya shigo cewa Hukumar Sauraren Koke-koke ta Jihar Kano, wadda ta fara binciken, a karkashin Muhyi Magaji, ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da binciken da ta fara.
Hukumar ta dakatar da binciken ne ganin yadda majalisar jiha ta yi katsalandan a cikin binciken. Idan za a iya tunawa, binciken hukumar ya tsaya ne kacokan a kan batun kudi, sabanin na majalisa wadanda zarge-zargen siyasa sun yi yawa a ciki.
Ko ma dai me sakamakon kwamitin Muhyi zai zartas, ba zai kai ga batun wata sabuwar tashin-tashina irin wadda gwamna ya umarci majalisa ta janye ba. Dama kuma Masarautar Kano ta fitar da amsar zarge-zargen da hukumar ta yi mata, wadanda kafafen yada labarai su ka watsa a lokacin da hayaniyar ta tirnike.
Idan ma ta yi zafi, watakila bai wuce majalisa ta kafa hujja da shi ta ce za ta kara yawan sarakuna a jihar Kano ba.