A daren jiya Alhamis ne wasu ‘yan kunan bakin wake suka kai hari dakin kwanan mata dake jami’ar Maiduguri jihar Borno.
Gidan jaridar PREMIUM TIME ta rahoto cewa akalla bamabamai biyu cikin uku da ‘yan kunan bakin waken suke dauke da su ne suka tashi a harin sannan kuma daya daga cikin su na dauke da bindiga kirar da AK47.
Abu Hanifa Babati shugaban kungiyan daluban jami’ar yace daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya tada bam din a kusa da sashen koyar da kula da dabbobi wato ‘Veterinary Medicine’ sannan kuma daya bam din ya tashi kusa da dakin kwanan mata.
Wani cikin mutanen da suka kwashe gawawwakin yace ‘’ ban da gawwawakin ‘yan kunan bakin waken da suka dauke babu wanda ya mutu amma masu gadin jami’ar hudu sun sami raunuka dabam dabam.”
Ma’aikatan hukumomin bada agaji na NEMA da BOSEMA sun riga sun kwashe gawawwakin ‘yan kunan bakin wake da suka mutu.