Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum yace majalisar wakilai bata da hurumin saka baki a binciken da majalisar keyi akan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
Dan majalisa Aliyu Sani Madakin Gini wanda shine yake wakiltar Dala a majalisar wakilai ya nemi majalisar da ta saka baki kan binciken da majalisar jihar take yi wa sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Kakakin yace ai ko sashen dokar da ta ba majalisa ikon iya yin haka sai har idan majalisar jihar ta kasa zama ne ko kuma akwa matsala a majalsar da ya hana ta zama. Amma yanzu suna zaman lafiya kuma kowa a majalisar ya amince da wannan bincike da suke yi akan Sarkin bai ga dalilin da za ace wai majalisar wakilai ta sa bakinta a kan binciken ba.
Rurum Yace cikin yan majalisa 35, 34 sun sa hannu lallai a binciki sarkin saboda haka bai ga inda za a ce wai majalisar wakila ta shiga cikin maganar ba.
Kuma kamar yadda yake a dokar kasa a sashe na 128, muna da ikon gudanar da bincike akan sarkin.
Discussion about this post