Samar da rigakafin cutar Kanjamau zai taimaka wa mutane – Hukumar NACA

0

Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya ce kasa Najeriya na kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar kanjamau ta hanyar tabbatar da cewa mutane da ke dauke da cutar sun sami ingantaciyar kular da suke bukata.

Sani ya fadi haka ne a taron wayar da kai da akayi a Abuja.

Sani Aliyu ya ce samar da alluran rigakafin cutar kanjamau na da mahimmanci domin hakan zai taimaka wajen rage yaduwar cutar musamman ga jarirai da ke kama cutar tun suna cikin uwayensu.

Bayan haka shugaban cibiyar bincike ta kasa da kasa kan cututtuka Alashle Abimiku ta tabbatar da cewa sashen binciken ta fitar da kyawawan sakamako akan kokarin da ake yi na samar da alluran rigakafin cutar kanjamau.

Alashle Abimiku ta kasashen duniya da yawa suna kokarin samar da allurar rigakafin cutar domin ganin a dakile yaduwar cutar.

Kasa Najeriya ce ta biyu da ta fi yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a duniya.

Share.

game da Author