Wani magidanci mai suna Sunday Adimagwu mai shekaru 56 da dansa Kenneth mai shekaru 21 suna ta kwanan da ‘ya kuma kanwan dan har na tsawon kusan shekara batare da daya daga cikinsu ya hakura ba.
Dan sandan da ya shigar da kara a kotun dake Ikeja jihar Legas Clifford Ogu ya ce Sunday wanda ke sana’ar tuki shi kuma Kenneth wanda dan kasuwane sun fara lalatane da yarinyar ne tun shekarar bara.
Clifford Ogu ya kuma kara da cewa yarin yar ta sami kanta ne a cikin wannan mummunar halin bayan mutuwar aure tsakanin mahaifiyar ta da mahaifinta.
Ya ce da yarinyar ta sami sarari sai ta gudu zuwa gidan mahaifiyarta inda ta fada mata duk abin da ke ta faruwa da ita a gidan ubanta.
Uwar yarinya kuwa bayan ta gama jin wannan mummunar labarin sai ta kai tsohon mijinta tare da dansa kara wajen ‘yan sanda inda aka shigar da kara zuwa kotun dake Ikeja a jihar Legas.
Alkalin kotun bayan ta gama sauraron su duka ne ta yanke hukuncin Uba da Da su biya kudin beli da ya kai Naira 250,000 sannan kuma da takardun shaidar biyan haraji guda biyu.
Daga karshe alkalin ta daga shari’ar zuwa 19 ga watan Yulin 2017.