Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Kwankwaso ne gwamnan da ya san ya fi sauran gwamnonin farar hular jihar aiki, tun bayan mulkin marigayi gwamna Abubakar Rimi.
Ganduje dai shi ne ya yi wa Kwankwaso mataimaki a tsawon shekaru takwas da Kwankwaso ya yi ya na mulkin jihar Kano, kuma shi ne ya gaje shi a 2015. Su biyu dai sabanin siyasa ya sa sun raba hanya,daya ya yi gabas daya kuma yamma.
Ganduje ya na magana ne a yau Litinin a wani taro don murnar cikar jihar Kano shekara 50. Wannan dai shi ne karo na farko da Ganduje ya yabi Kwankwaso a karon farko a cikin bainar jama’a, tun bayan samun rashin jituwa a tsakanin su.
Ya jinjina wa Rimi wanda ya yi gwamnan Kano a zamanin jamhuriya ta biyu, a karkashin jam’iyyar PRP tsakanin 1979 zuwa 1983. Ganduje ya ce Rimi ya gina harsashin ci gaban Kano, ta hanyar gudanar da ayyukan ci gaba a cikin shekaru hudu da ya yi ya na gwamnan Kano.
Ganduje ya lissafa wasu muhimman aiyukan Rimi da suka hada kafa gidan talbijin mallakar jihar, CTV, jaridun Triumph, hukumar kula da aiyukan noma da raya karkara, wato KNARDA da KASCO da hukumar bada wutar lantarki a karkara da sauran su.
Rimi dai ya sauka daga gwamnan jihar Kano, bayan ya canja sheka daga PRP ya koma NNP, wadda ya tsaya mata takara, amma ya fadi zabe, inda Sabo Bakin Zuwo na PRP ya kada shi a 1983.
“Dalilin da ya sa na zabi Kwankwaso a matsayin na biyu kuwa, saboda ko ma dai mene ne a tsakanin mu, a zangon farko ya kawo muhimman ayyuka, kuma ya bude hanyoyi tsoffi da kuma kirkiro dimbin sabbin hanyoyi da suka rike bullewa ta wasu yankuna, unguwanni ko hadewa da wasu manyan tituna.” Inji Ganduje.
Ya kuma ce Kwankwaso ya yi wadannan ayyuka ne a daidai lokacin da ya ke fuskantar babban kalubalen malaman addinin musulunci wajen ganin an kafa shari’ar musulunci a Kano, tsakanin 1999 zuwa 2003.
Ganduje ya ce a lokacin an yi ta shirya wa Kwankwaso tuggu, makarkashiya da kutunguilar neman a raba shi da mulki, a lokacin da ya ke ta kokarin habbaka jihar Kano ta ci gaba. Wannan ne ya sa bai yi tazarce ba, inji Ganduje.
Ya jaddada cewa Kwankwaso bakin rai bakin fama ya ke harkokin sa, shi ya sa ya tsaya tsayin daka ya fito da fitar sa a yinkurin komawa kan mulki da ya yi a 2011, kuma ya yi nasara. Wannan ne ya sa har gobe Kwankwaso ya kasance gwani na. Inji Ganduje.