Zaman Jamila da Ahmed Musa dai ya ki daidaituwa tun bayan dukan tsiya da take sha a wurin sa.
Ahmed Musa ya auri wata masoyiyarsa mai suna Juliet Adeh Ejue a wata kotu a Abuja.
Jami’an ‘yan sandan Britaniya sun taba tuhumar Ahmed Musa kan zargin lakada wa matar sa Jamila dukan tsiya a kasar.
Ahmed Musa dan wasan kungiyar kwallon kafan Leicester City ne.
Kamar yadda wata jaridar kasar Britaniya mai suna theSun.co.uk ta rubuto labarin a wancan lokacin ta ce jami’an ‘Yan sanda sun ziyarci gidan Ahmed Musa da karfe 1 na safen ranar domin gudanar da bincike akan hakan.
Jami’an ‘yan sandan sun dauki bayanai daga bakin tsohowar matar sa Jamila, da ‘ya’yan sa biyu, Ahmed da Halima.
Jami’an ‘yan sandan sun tabbatar da tsare Ahmed Musa a wancan lokacin.