Da sanyin safen yau ne akayi jana’izan uwargidan marigayi Aminu Kano wanda akafi kira da Shatu a Kano.
Aisha ta rasu bayan jinya da tayi ta fama da shi.
Ahmed Mukhtar daya ya tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar marigayiyar yace Shatu ta dade bata da lafiya kafin Allah ya dauki ranta yau.
Shatu ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da wadansu manyan yan siyasar Kano sun halarci jana’izan marigayiyar da akayi a gidan Sani Kabara, Tukuntawa hanyar Shagari Quaters.
An rufe ta a makabartar Dandolo da ke Kano.
Discussion about this post