Yin gwajin cutar Hepatitis shine hanya mafia sauki wajen rage yaduwar sa

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce gwamnatin Najeriya na kokarin rage yaduwar cutar dake kama huhu wato Hepatitis a kasa.

Darektan aiyukan asibitoci Joseph Amedu wanda ya wakilci ministan ya fadi hakan a taron da kungiyar likitocin Najeriya ta shirya don wayar da kan mutane akan cutar wanda aka yi a Abuja mai taken

‘’Mu kawar da cutar Hepatitis daga kasa Najeriya’’.

 Ministan ya bayyana cewa cutar Hepatitis cuta ce da take kama huhu wanda ake kasa gane shi da wuri har sai ta yi wa mutum illar da ko asibiti aka kai mutum da kyar ya ke sha.

Ya kuma kara da cewa hakan na iya faruwa ne ga mutum ne Idan ba a yi gwaji da wuri ba.

Bayan haka wani likita mai suna Chukwuma Anyaike ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ci gaba da wayar da kan mutane akan illolin da ke tattare da cutar tare da samar da ingantattun alluran rigakafin cutar.  

‘’Za mu iya kawar da cutar Hepatitis daga kasa Najeriya idan aka sa ido wajen ganin jarirai ba su kamuwa da cutar tun suna cikin uwayensu’’

‘’Sauran hanyoyin kawar da cutar sune yin alluran rigakafin cutar sannan kuma da kare juna musamman wajen yin amfani da kororo rota wajen saduwa da Juna’’.

Daga karshe shugaban kungiyar likitocin Najeriya Tony Philips ya shawarci mutanen Najeriya da su yawaita ziyartar asibiti domin yin gwaji akan cutar.  

Share.

game da Author