Gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki sabin malaman firamarin 1000 domin shawo kan matsalar karancin malamai da makarantun gwamnatin jihar ke fama da shi.
Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da hakan a bukin taron ranar zagayowar ma’aikatan da aka yi a jihar.
Ya ce wadanda da suke da shaidar kamala karatu na NCE ne kadai za’a dauka aiki maluntar.
Mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakkala wanda ya wakilci gwamna Yari ya ce hakan zai samar da aikin yi wa matasa wadanda suka kamala karatunsu kuma suke zaman kashe wando a jihar.
” Gwamnatin jihar Zamfara ta amince tsakanin ta da kungiyar ‘yan kwadigon jihar cewa za ta biya kudaden ma’aikatan gwamnatin da suka ajiye aiki da ya kai Naira miliyan 100”.
”mun kuma amince da mu kafa kwamitin da za ta samar da hanyoyin da za a iya biyan mafi karancin albashi wa ma’aikatan da suka yi ritaya”.
Shugaban ‘yan kwadugon jihar Zamfara Bashir Marafa a nashi tsokacin shima ya jinjina wa gwamnatin jihar Zamfara akan kokarin da take yi wajen biyan bukatun ma’aikatan jihar.