Yadda Kamfanoni suka yi ta yi wa asusun bankunan Babachir zubi da kudaden da aka tarawa ‘yan gudun hijira

0

Kamar yadda rahotan majalisar dattijai ya nuna da kuma bayanan da muka samu daga Babban bankin Kasa CBN da ma’akatar yi wa kamfanoni rijista CAC, Sakataren gwamnatin tarayya ya yi amfani da wasu kamfanoni domin ya rarraba kudade da bada kwangilolin karya ga wadansu da basu da cikakken lasisin gudanar da irin wadannan kwangiloli da kuma wadansu na kusa dashi.

Dalilin yin hakan shine domin wasu daga cikinsu su dinga biyan sa kwamisho, wato wani kaso daga cikin kudaden kwangilolin.

Bayan Babachir ya karbi kudaden aikin daga PINE akalla kamfanoni biyar kuma sun biya shi naira miliya N450 a wata asusun banki na Eco Bank (182001809) wanda mallakar kamfanin Rholavision Engineering dashi Babachir ke da mallaki da wata asusun sa na Diamond (0003004417).

Kamar yadda bayanai daga babban bankin Najeriya suka nuna, Babachir ya na daya daga cikin masu mallakin kamfanin Rholavision har zuwa watan 15 ga watan Fabrairun 2017 wanda hakan ya saba wa dokar kasa a matsayinsa na babban jami’in gwamnati.

Kamfanin Josmon Technologies sun saka naira miliyan 317 a asusun wannan kamfanin daga watan Maris 29 zuwa April 20, 2016.

Ko a lokacin da aka ba kamfanin Rholavision kwangilar cire ciyawar, Babachir wanda shine mai mamallakin kamfanin yana sakataren gwamnatin tarayya wanda hakan ya saba wa dokar kasa Najeriya.

A watan Agustan 2016 kamfanin JMT Global ta tura naira miliyan 30 daga asusun Zenith zuwa asusun kamfanin Rholavision a dalilin wasu kwangiloli da suka samu da za su yi a jihar Adamawa na naira miliyan 199.4.

Haku itama kamfanin gina rijiyoyin burtsatse na ‘Adamawa Boreholes and drilling Companies’ sun tura wa kamfanin Rholavision naira miliyan 18 kason sa na kwangilar da suka samu na gyaran wasu ajujuwa bakwai na makarantar mata Yeskule da ke Michika.

Haka kuma kamfanin ‘Barde Brothers’ suma sun biya Rholavision naira miliyan 71 a matsayin kason kamfanin na kwangilar da suka samu na gina ajujuwa bakwai a jihar Adamawa a watan Oktoban 2016. Bayan haka kuma sun tura naira miliyan 13 zuwa asusun sakataren gwamnatin tarayya din a watan Satumbar 2016.

Bayan kamfanonin da suka yi ta biyan Babachir kudade a matsayin kason sa akwai wasu kuma da yawa da suka karbi wadannan kwangiloli daga PINE ta hanyar da bai dace ba wanda hakan ya saba wa dokokin bada kwangiloli.

Yanzu dai Babachir na fuskantar wata kwamiti da shugaban kasa ya kafa domin binciken zargin da rahoton da kwamitin majalisar dattijai tayi akansa.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne yake shugabantar kwamitin.

Share.

game da Author