Jihar Kogi ta sami kyatar gidajen sauro sama da miliyan 2 daga USAID

0

Kungiyar kula da cigaba na kasa da kasa na kasar Amurka USAID ta tallafa wa gwamnatin jihar Kogi da gidajen sauro sama da miliyan biyu domin rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a jihar.

Darektan kungiyar Nancy Lowenthal ta dankawa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello wannan gidajen sauron tare da wasu kudaden da ya kai dala miliyan 1.1 domin wayar da kan mutanen kananan hukumomi 21 dake jihar akan mahimancin amfani da gidajen sauron.

Gwamnan Yahaya ya gode wa USAID da irin wannan taimako da ta kawo jihar sannan yayi alkawarin ganin cewa jihar ta yi amfani dasu yadda ya kamata.

Share.

game da Author