Za’ a bude Filin jirgin saman Abuja gobe

0

Hukumar kula da safarar jiragen sama ta kasa ta sanar da bude filin jirgin saman Nnamdi Azikwe gobe Laraba 19 ga watan Afrilu 2017.

Shugaban hukumar Ahmed Usman ne ya sanar da hakan bayan gamsuwa da Hukumar ta yi da ayyukan da aka gudanar a filin jirgin saman.

An rufe filin jirgin saman Abuja ne saboda gyara da ta ke bukata.

A tsawon makonnin da akayi ana aikin safarar jiragen sama ya koma Kaduna.

Matafiya sai sun tafi Kaduna kafin su hau jirgi zuwa wasu sassa na kasar nan.

Share.

game da Author