Hukumar kula da kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya WHO ta yi kira ga kasashen da ke tasowa da su kara yawan kudaden da suke warewa domin samar da tsaftatacen ruwan sha da kuma kula da muhallin su.
Hukumar ta ce hakan zai sa ta samu nasara akan burinta na ganin hakan ya yiwu wanda yake kunshe a cikin shirye shiryenta na ‘Sustainable Development Goals (SDG)’ zuwa shekara 2030.
Hukumar ta sanar da cewa wadannan kasashen ba su samar da isassun kudaden da ake bukata domin ganin cewa mutane sun sami tsaftatacen muhalli da ruwan sha.
Hukumar ta kuma shawarci wadannan kasashen akan yadda da za su iya cin ma burinsu wanda ya hada da fara tattalin wadanan kudaden ko kuma su kirkiro wasu hanyoyin da za su sami kudaden da suke bukata tun da wuri.
“ Kamata ya yi wadannan kasashen su kara yawan kudaden da suke warewa domin ya fi dala biliyan 114 da suke samarwa don samun nasarar hakan.”
Bayan haka bincike ya nuna cewa mafi yawan mutanen kasa Najeriya na fama da karancin ruwan sha.
Binciken ya kuma nuna cewa mutanen da suke zaune a biranen kasar na samun tsaftatacen ruwan sha ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse inda wasu ke samun irin wadannan ruwan ta hanyar siya daga inda ake samo tsaftacaccen ruwa.
Amma mafi yawan mutanen da ke zaune a karkara na samun ruwan shansu daga kududufi ko rafi ne.
Darekta a hukumar WHO Maria Neira a nata tsokacin ta ce akalla mutane miliyan 2 ne a kasa Najeriya ke amfani da ruwan da ba shi da tsafta wanda hakan yakan sa a kamu da cututtuka irin su amai da Zawo, gudawa, cutar shan inna da sauransu.
“Bincike ya nuna cewa amfani da ruwan da ba shi da tsafta na kawo cutar amai da gudawa wanda ke sanadiyar mutuwan mutane 500,000 a kowace shekara.”
A binciken da hukumar ‘Water Aid Nigeria’ ta yi ya nuna cewa sama da miliyan 63 na mutanen Najeriya ba su da zabi wajen samun ruwan da suke amfani da shi sannan kuma a kowace shekara yara kanana ‘yan kasa da shekara 5 na rasa rayukansu saboda rashin tsaftatacen muhalli da ruwa sha.
Wani jami’i mai kula da sashen ruwa na majalisar dinkin duniya Guy Ryder yace wannan matsalace wanda ya kamata duniya gaba daya su hada kai domin magance ta.
“ Idan har aka samu aka iya samar da mutane da yawa da ke fama da wadanna matsaloli za su sami waraka akan hakan sannan kuma zai sa a sami nasara akan kokarin ganin cewa an sami ingantacciyar kiwon lafiya musammman a irin wadanna kasashe da suke fama da hakan sanna kuma za a wadata matasa da aikin yi da sauransu.”
Da ga karshe Guy Ryder ya ce idan har aka samu nasara akan wadannan shirye-shirye mutane za su sami tsaftacaccen muhalli da ruwan sha domin zama cikin koshin lafiya.