Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ce daya daga cikin abubuwan da ke bashi takaici shine idan ya tuna dakile shirin gina alkaryar shirya fina-finai da akayi wanda da za’a yi a jihar Kano.
“ Na yi bakin ciki da ba a gina Film Village a Kano ba, amma na yi farin ciki da aka ce a yanzu a jihar Kaduna ne za a kafa shi.”
‘’Da an gina Film Village a Kano, dimbin matasa masu basira da fasaha za su samu aikin yi. Inji Sarkin. Ya kuma yi tsokaci, kuma ya nuna irin yadda ake wa wasu abubuwa fahimta ta daban.
“A Kano ne fa aka samu mutumin da ya yi ilimi, ya yi karatun jami’a, amma ya jagoranci gangamin kone littattafai, wai don na soyayya ne.” Sarkin yace haka ta faru a cikin al’ummar da ke fama da matsalolin da suka shafi auratayya.
Ca da akayi wa shirin a wancan lokacin ne ya sa aikin bai yuwu ba kuma.