Samar wa Makiyaya matsuguni zai taimaka wajen kawo karshen yawan rikin Makiyaya da Manoma

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afirika, ECOWAS, da ta taimaka ma Najeriya a kokarin da takeyi na ganin ta kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da Manoma.

Gwamnan ya ce shigowa da kungiyar ECOWAS cikin wannan kokari na gwamnati zai taimaka wajen ganin an samu dawwamammiyar jituwa tsakanin Fulani da makiya musamman a jihohin Taraba, Kaduna Benue.

Ganduje ya fadi hakan ne da yake karban bakuntar kungiyar makiyaya na Miyetti Allah MACBAN a fadar gwamnatin jihar Kano.

Ya sanar wa bakin sa cewa kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriya ta amince cewa mafi yawan makiyaya da ke ta da zaune tsaye a yankin ba ‘yan Najeriya bane, kusan dukkansu sun fito ne daga kasashen Nijar da Chadi.

Ganduje yace dole ne gwamnati ta samar da hanyoyin da za’a bi wajen wadata makiyaya da matsuguni na dindindin saboda yawace yawacen su ne ke kai su ga fadawa gonakin manoma da dabbobinsu.

Ya ce hakan zai canza rayuwarsu musamman ta fannin ilimi, cudanya da mutane da kuma samun dabarun zamani kan yadda zasu kiwata dabobin su.

Ya yi bayanin matakan da gwamnatin sa ta dauka domin samar wa makiyaya matsuguni a yankin da ya hada da:

1. Kebe wasu kauyuka da wadatar da su da ababen more rayuwa domin makiyaya su sami matsugunin da zasu kiwata dabbobinsu sannan a koyar da su dabarun kiwo na zamani.

2. Gwamnatin jihar Kano za ta samar da kasuwannin cinikin dabobi na zamani domin samar wa dabbobin daraja.
Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan hubbasan da yayi na kafa wata kungiya mai zaman kanta domin sasanta tsakanin makiya da manoma mai suna Pastoral Resolve PARE.

Da yake bada na shi bayanan shugaban kungiyar makiyaya Muhammadu Zuru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da wata shiri da zai wayar wa manoma da makiya kai akan illar rashin zaman lafiya a tsakaninsu.

Zuru ya godewa gwamna Ganduje akan kokari da gwamnatinsa ta keyi wajen ganin ta samar wa manonan mtsuguni na dindindin da kuma labi da zasu dinga bi wajen kiwon dabbobinsu.

Babban jami’in ma’aikatar koyon aikin gona ta tarayya Muhammad Abubakar ya kara tabbatar da cewa ma’aikatar sa na iya kokarin ta wajen ganin ta inganta rayuwar makiyaya sannan kuma ya shawarce makiyayan da su dauki kiwo a matsayin aiki ne na musamman amma ba al’ada ko wani abu da sai sunyi don sun gada.

Share.

game da Author