Ambaliyar Almajirai A Kano: ’Yan Nijar sun fi yawa

0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa, ‘yan Nijar ne mafi yawan almajiran da suka yi katutu suna garari a Kano.

Ya kuma kara da cewa akwai wasu da yawa da suka fito daga wasu kasashe makwabta na nan Afrika ta yamma.

“Daga wani kwakkwaran bincike da muka yi, mun gano cewa yawancin almajiran nan daga cikin miliyan ukun da ke Kano, sun fito ne daga kasashen Nijar, Chadi da Arewacin Kamaru da wasu kasashe na Arewa maso Yamma.”

Da yake magana wajen taron shirin farfado da tattalin arzikin jihar Kaduna, Ganduje yace wadannan almajirai babbar matsala ce ta zamantakewar al’umma da kuma tattalin arzikin kasa.

“Idan za mu iya haduwa mu fuskanci wannan matsala bai-dayanmu, kuma mu fito da wata kwakkwarar doka ta bai-daya, wadda za ta hana kwasar kananan yara daga wancan gari zuwa wannan, to ina ganin yin hakan zai sa jihohi su shawo matsalar almajirancin nan.”

Ya ci gaba da cewa matsalar almajiranci abu ne da ya ke addabar jihohin arewa, kuma ya zame musu karfen-kafa. Ya ce ya zama dole jihohin nan bakwai su gano alfanun tattalin arzikin da zai fitar da su daga matsanancin halin da su ke ciki.

“Wannan ne karo na farko tun bayan dawo da mulkin dimokradiyya cikin 1999, inda aka samu gwamnonin jihohi bakwai na Arewacin kasar nan suka yanke shawarar zaunawa su nemo mafitar da za a bi domin ficewa daga tabarbarewar tattalin arzikin da yankin ke fama da shi.”

Share.

game da Author