Makomar ‘yan Matan Chibok da sauran kalubalen da muke fuskanta, Daga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

0

Yayin da a yau mu ke juyayin cika shekaru uku bayan sace ‘yan matan Chibok, ya kamata kuma mu tuna da cewa wadannan mata kadan ne fa daga cikin dimbin mutanen da barnar Boko Haram ta tarwatsa ko ta kassara. Ina yin kira ga kungiyar ceto ‘yan matan Chibok da ta fadada kungiyar, su hada har da batun sauran kananan yara mata da maza wadanda Boko Haram ya illata ko ta sace. Da kuma fafutikar jawo hankali wajen duba matsalar da ‘yan matan gaba daya ke ciki a wannan yanki.

Bari na ba ku wani karin haske dangane da yadda wannan matsala ta yi katutu a yanzu. Ya zuwa yau, a sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori 2, akwai ‘yan mata sama da 1500 wadanda Boko Haram su ka yi fashin su, duk sojoji sun kwato su, amma daga mai ciki sai mai goyo a cikin su. Ana kuma ci gaba da daukar yara kanana zuwa inda babu wanda ya san wurin da ake tafiya da su, saboda al’umma sun ki su maida hankali wajen magance wannan matsala.

Ashe ya na da kyau kwarai kuma babban kalubale ne ga kungiyar nan ta neman a dawo da ‘yan matan Chiobok, su kara kaimi wajen neman goyon bayan jama’a, wajen buga wa al’umma misalin halin kuncin da ‘yan matan Chibok ke ciki, amma fa kada su tsaya kacokan a kan fafutikar neman ceto wadannan ‘yan mata kadai. Bukatar mu ita ce a samu nasarar dawo da duk wata yarinya da ke hannun Boko Haram, ba su kadai ba. Amma akwai sauran rina a kaba fa, bayan an dawo da wadannan mata, sai mu tambayi kan mu shin a ina za a dawo da wadannan mata ne? A cikin wace al’umma za su dawo? Shin rayuwa a cikin wannan al’umma ta zarce rayuwa a cikin sansanonin gudun hijira?

Wadannan tambayoyi tabbas sun sa tilas mu yarda gaskiyar magana cewa irin al’ummar da muka wanzar wa kanmu ita ce ummul haba’isin bayyanar kungiyoyi irin su Boko Haram da kuma sauran bala’o’in da suka biyo baya irin na sace ‘yan matan Chibok.

A duk tsawon rayuwa ta, na kasance ina cikin fafutikar nemar wa mata hakkokin da al’umma ta tauye musu, ko kuma magance matsalar mayar da su koma-baya a cikin al’umma. Na kuma yarda da cewa akwai hatsari sosai ga duk wanda ya jajirce a kan wannan matsayi a cikin al’ummar mu. Su kuma masu ilminmu sun ki daukar wannan matsala da muhimmanci, ta hanyar kau da kai da yin gum da bakin su dangane da wannan matsala.

Babban abin da ke damunmu shi ne, don me za mu tsaya mu maida kai wajen matsalolin da suka shafi rayuwar matan karkara, tunda za mu iya bai wa namu ’ya’ya matan mafificin ilmi a ko’ina ne cikin fadin duniya? Don me za mu dauki mudubin da zai nuna mana irin mummunar rayuwar kuncin da muka jefa mafi akasarin al’ummarmu?

Su fa masu ilmin mu da sauran manya ba su so su ji ana kawo musu kididdigar halin kuncin da al’umma ke ciki. Kwanan nan na yi wani jawabi inda na ce yankin Arewa-maso-Gabas da Arewa-maso-Yamma na Nijeriya ya fi ko’ina fama da talauci a cikin kasar nan. To wannan jawabi ne har ya haifar da cece-ku-ce mai zafi. Har yanzu ba a daina surutai a kai ba. To amma mene ne gaskiyar wannan kididdiga ne? Kungiyar OPHI tare da ta Majalisar Dinkin Duniya ce a cikin 2015 ta buga wannan bayani, inda ta ce kusan kashi 46 na ’yan Nijeriya duk su na cikin fama da talauci.

An bayyana wannan kididdiga ne fa a bisa wani binciken kwakwaf da hukumar bin diddigin fatara da talauci a duniya da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar. An gudanar da binciken ne ta hanyoyin amfani ko maida hankali ga matsayin ilmi, kiwon lafiya da kuma matsayin rayuwar al’umma. Duk da cewa wannan kididdiga ta yi muni, ta kara bayyana bambanci da tazarar talaucin da ke tsakanin wannan yanki da wancan da kuma tazarar da ke tsakanin maza da mata.

Misali, a Kudu-masu-Gabacin kasar nan wadanda ke fama da kuncin talauci ba su kai kashi 20 bisa 100 ba, amma wadanda ke fama da talauci a yankin Arewa-maso-Gabas sun kai kashi 76.8 cikin 100. Yayin da kashi sama da 80 cikin 100 na Arewa-maso-Yamma ke fama da talauci. Sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummar jihohin Yobe da Zamfara ne ke fama da talauci, idan aka kwatanta da kashi 8.5 kacal nasu fama da talauci a jihar Legas da kuma kashi 11 bisa 100 na al’ummar jihar Osun da na Anambara.

Wannan jawabi ya janyo aka rika yi mini rubdugun zafafan kalamai a kan ni kai na, aka saki batun da na ke magana a kai don kawai ana son na daina bayyana irin wadannan matsaloli. Akwai wadanda suka yi amanna cewa wannan rubdugu da ake yi mini zai iya zubar min da kima. To idan haka din ake nufi, ai ba za su yi nasara ba ta hanyar suka da yi min karairayi a kafafen sadarwa na intanet.

Masu yi min wannan rubdugu sun saki maudu’in da ake magana a kai, wanda ba ni kadai ba, dukkanmu da ke da hakki a cikin wannan fafutika, ya kamata mu tuna wasu abubuwa. Muna mabana ne a kan wata al’umma da ke adawa da kaifin ilmi da kuma wasu mutane wadanda su ne suka haddasa mana wannan matsalar tsaro abin da ya haifar da wannan kakkausan martani ga shawarar da na bayar.

Abu na biyu shi ne, duk wadannan matsaloli da ake magana a kai, su na nan damfare a yankunan mu da dadewa suka yi mana katutu. Shi ya sa canja tunanin mutane abu ne mai wahalar gaske da kuma matukar ciwo. A karshe, kada mu sake mu biye wa masu adawa da mu, gaba dayanmu mu dulmiya a cikin kwatami daya. Duk abin da mutum zai fada, ya je ya fada.

Maimakon mu boye wannan kididdiga, abin da ya kamata shi ne mu kara fito da wannan matsaloli a sarari. Duk abin nan da na bayyana ba ni ne na kirkire su ba, su na nan duk mai so zai iya shiga ya duba ya gani. Kawai dai ba a taba fito da su fili an bayyana su ba ne, sai yanzu. Amma dai wannan kidaiddiga ta taimaka mana sanin irin yadda fatara da talauci suka yi wa mata da kananan ’yan mata katutu.

Bayanin kididdigar ya bayanna cewa:

Sama da kashi 70.8 na matan da ke Arewa-maso-Yamma ba su iya karatu da rubutu ba, idan ka kwatanta da kashi 9.7 kacal na matan da ke yankin Kudu-maso-Yamma.

Sama da kashi 2 bisa 3 ‘yan mata ‘yan shekaru 15 zuwa 19 na Arewa, ba su iya karanta jimla daya tal, idan aka kwatanta da kashi goma ne kawai ba su iya karanta jimla a yankin Kudu.

Sama da kashi 80 na matan da ke cikin wasu jihohi takwas na Arewa, ba su iya karatu da rubutu ba.
Kashi hudu ne kacal na matan Arewacin kasar nan suka kammala karatun sakandare.

Kashi 78 bisa 100 kananan ‘yan mata na gidan miji a Arewa-maso-Yamma, yayin da a Arewa-maso-Gabas sun kai kashi 68 cikin 100, sai 35 cikin 100 na Arewa-ta-Tsakiya. Wannan kididdiga kai tsaye ta hasko mana yankin da talauci ya fi yi wa katutu a kasar nan. Yayin da a yankin Kudu-maso-Kudu, 18 cikin dari ne kadai ba su iya karatu da rubutu ba, sai kashi 17 a yankin Kudu-maso-yamma sai kashi 10 kacal a yankin Kudu-maso-gabas.

Baya ga asarar da muke yi masu yi mana ayyukan gina kasa da kuma rashin samun kudin shiga sakamakon rashin alkibla da maida kai a fannin ilmi, musamman ga yara mata, hakan ya haifar da babbar matsalar zamantakewar rayuwa da kuma matsalar kiwo da kula da lafiya. A cikin kowane minti 10, mace ‘yar Nijeriya daya na mutuwa a wurin haihuwa. Arewa-maso-Gabas ne aka fi samun mutuwar mata yayin haihuwa da ta kai mace 15,000 na mutuwa a wurin haihuwa daga cikin mata 100,000. Wannan kididdiga ta nunka ta sauran kasashen duniya sau biyar.

Wannan kididdiga ta fito da gaskiyar da mafi yawanmu ba mu son a fadi. To tilas ne fa mu yi watsi da al’adar tsuke baki a yi shiru. Akwai matsala a tattare da mu. Ko kuma ma na ce rudani. Dukkanmu a wannan kasa, tun daga ’yan siyasa, masu ilmi, Sarakuna da sauran masu sarautun gargajiya da shugabannin addinai da ’yan kasuwa da kungiyoyin sa-kai – tilas mu hadu mu magance wannan matsala. Masu kaunar Arewa na gaskiya su ne wadanda suka yarda akwai wadannan matsalolin, kuma suka jajirce wajen son a canja.

Ba karamin abu ba ne zai iya faruwa idan muka yi watsi da magance wannan matsalar, ina mamakin shin ko jama’a sun kula da haka. Akwai yiwuwar yara kashi 50 da iyayensu mata ke da ilmi za su iya rayuwa sama da shekaru biyar.

Sannan kuma iyaye mata masu ilmi ke da jajircewa tura ‘ya’yansu makaranta.

Jirajiran da iyayen su mata ba su kai shekaru 18, su ne ke da kashi 60 cikin 100 na yiwuwar mutuwar a cikin shekarar farkon haihuwar su. Amma kashi 19 ne kadai daga cikin 100 na ‘ya’yan iyaye masu shekaru 19 aka yi kirdadon ka iya mutuwa a shekarar farkon haihuwr su.

Sannan kuma karamar yarinyar da ta haihu ta na da shekaru 15 a kasashen da ke fama da talauci, sun fi saurin mutuwa a wurin haihuwa da kuma saurin kamuwa da ciwon yoyon fitsari fiye da manyan mata, wato sun ma nunka. Yara mata masu kasa da shekaru 15 ta fi saurin mutuwa a yayin haihuwa kusan sun nunka mata masu shekaru 20 sau biyar wajen saurin mutuwa a wurin haihuwa.

Wadannan bayanai na nunawa kuru-kuru cewa rayuwar dan adam a wannan yanki ta na cikinhadari. Matsalar ta fi yin katutu a yankin arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas. Ko da ya ke shi ma yankin Arewa-ta-Tsakiya ya zarce yankin Kudu muni.

Ina kara jaddada cewa matsalolin da mata fa ke fuskanta ya zarce matsalar ilmin ’ya’ya mata, auren wuri da kuma talauci. Har yau su kan su mata masu ilmi sun a fuskantar matsalar rashin samun damammaki daidai da maza a wuraren aiki da sauran wasu matsaloli na bambancin da ake nunawa tsakanin maza a kan mata.

A lokacin da na ke Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, na tilasta sauran bankuna sun rika daukar ma’aikata mata daidai da yawan ma’aikata maza zuwa 2014. Sannnan kuma mun samar da damar daukar kashi 40 bisa 100 na manyan jami’an Bankin Tarayya da sauran bankuna su kasance mata ne. Sai kuma kashi 30 bisa 100 na Hukumar Daraktoci na Bankin Tarayya da sauran bankuna, mata ne.

A nan, ina so na sake jaddadawa jama’a cewa ba sai yanzu da na zama Sarki ba ne na fara yin batun samar wa mata damammaki a fannonin rayuwa daban-daban. Haka kuma kyamar da na ke yi wa auren-dole, dukan mace, sakin-wulakanci ga mace da sauran su, ba sabon abu ba ne. kuma ba wani salon adawa ce ga wani ko wata kungiya ba.

Muna ikirarin mun firgita sosai dai bala’in Boko Haram. Muna cewa dabbanci ne. Sun gudu da kananan yara mata, sun raba su da makarantar su, sun tilasta aurar da su a kan sub a tare da amincewar su ba. Sun musu ciki, sun maida su iyaye tun sun a kanana. Sun kuma haifar musu da cututtuka, watakila har ma da barazanar duka da zagi na kaskanci.

To mun ji wannan abin ya tayar mana da hankali. Sai mu tsaya mu yi tunani. Shin wannan abin da ya same su, ba ya faruwa ne a kullum a cikin kauyukan Arewacin Nijeriya da wasu yankunan Kudu? Ba a samun yara mata da ba su kammala karatun su? Ba a yi musu auren dole tun su na kanana? Ba a gallaza musu?

Duk wanda zai fito ya kalubalanci wani tsari ko ya ke nema wa marasa karfi hakkin su, to dole ya shirya wa fuskantar suka da kushewa da kokarin bata masa suna, razanarwa ko shirya masa makirce-makirce.

Share.

game da Author