Mutanen garuruwan da ambaliya da goguwar iska ta afka wa dake karamar Hukumar kura suna kira ga gwamnatocin Arewa da hukumar bada agajin gaggawa da su kawo musu dauki akan iftilain da ya same su.
Mutanen garuruwan Danga, Tofa, Iyatawa, da Yadagungume dake karamar hukumar Kura, jihar Kano ne wannan jarabawa ta fada ma.
Gidaje sama da 150 ne suka rushe a sanadiyyar wannan ruwan sama in da ka rasa ran wani yaro dan shekara 15.
Mutanen yankin suna kira ga gwamnatoci da masu hali da su kawo musu dauki, su agaza musu domin farfadowa daga wannan jarabawa da su ka fada.
Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar Kura, Alhaji Barau Salisu ya yi kira a madadin mutanen yankunan ga Jama’a musamman masu hali da su kawo taimaka wa mutanen garuruwan da wanna abu ya faru da su.
“ In kira ga attajirai da gwamnatoci da su kawo ma wadannan mutane taimako. Da yawa akan taro a wuri daya ne a kwana saboda babu gidajen duk sun rushe.”