Wata kotun a jihar Edo ta daure wani mutum mai suna Friday Azala bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘Yar abokin sa fyade a gidansa.
Yarinyar ‘yar shekara 12 ne.
Wanda ta shigar da kara ta ce Azala ya danne yarinyar ne har sau biyar da karfin tsiya yana lalata da ita.
Ta ce yakan rude ta da kudi wajen kiranta zuwa gidansa.
Duk da cewa an tabbatar da hakan a kotu, Azala ya karyata wannan zargi in da yace bai taba kwana da ita ba sai dai ya taba rungumar ta har sau biyar.
Alkalin kotun ya ce a ci gaba da ajiye Azala a kurkuku har sai zaman kotun na gaba.