Kawo Sadiq Zazzabi Kurkuku rahama ce a garemu, domin sanadiyyarsa mun fito – Inji wani tsohon fursina

0

Bayan kwanaki bakwai da shahararren mawakin nan Sadiq Zazzabi yayi a kurkuku, ya fito bayan kotu ta bada belin sa.

Da yake kurkuku a wancan lokacin Sadiq ya hadu da wasu fursinoni da abinda ake nema a wajensu domin a sake su bai taka kara ya karaya ba.

Bayan ya fito ya koma domin taimakawa wadanda suke bukatar irin wannan taimako domin a sake su.

A hirar da yayi da gidan jaridar PREMIUM TIMES Sadiq Zazzabi yace da yawa daga cikin wadanda su ke neman taimakon an kama su ne ba tare da sun aikata wani laifi ba.

‘Wasu an kama sune a lokacin da jami’an tsaro suka kai samame wasu unguwanni sai tsautsayi ta hau kan su.”

‘’Da yawa daga cikinsu suna bukatar biyan tara ne wanda wasu 10,000 kawai suke bukata.

“ Wani mai teburin shayi ya fada irin hakan inda jami’an tsaro suka kama shi bai jiba bai gani ba.

Wani mai suna Manu Sambo ya fada wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa bai san hawa bai san sauka ba sai kwatsam jami’an tsaro suka hada da shi a wata samame da suka kai da dare lokacin shi kuma ya na dawo gida daga sana’ar sai da takalma da yake yi.

Manu yace “Allah ne ya turo mana Sadiq Zazzabi domin ya fitar damu daga wannan kangin domin kusan dukkan mu da muke nan tara ne kawai za mu biya kuma bamu dashi sai da Allah ya Kawo mana Sadiq.

Hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano ta maka Sadiq a kotu saboda zargin fitar da wakar da ya rerawa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ba tare da ta amince masa ba.

Karanta hirar a shafin mu na Turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-XhM

Share.

game da Author