Hukumar da ke kula da ayyukan rundunar tsaro na farar hula, Civil Defence, hukumar kashe Gobara, hukumar shige da fice da na kula da kurkukun kasa ta dakatar da wasu manyan jami’an hukumar kula da kurkukun kasa su uku saboda hannu da suke dashi dumu-dumu wajen sakin tsohon gwamnan jihar Adamawa James Ngilari daga kurkukun da yake tsare.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Peter Tenkwa, Abubakar Abaka da John Bukar.
Kakakin hukumar kurkuku ta kasa Francis Enobore ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya saka wa hannu yau.
Alkalin babban kotu da ke jihar Adamawa Nathan Musa ya bada belin James Ngilari a makon da ya gabata bayan wadata ta da takardun karya da akayi wanda yake nuna cewa wai tsohon gwamnan bashi da isasshen lafiya kuma a dalilin haka alkalin yaba da belin sa.