A ranar Talatan nan ne majalisar wakilai ta dakatar da tattaunawa akan wasu kudirori shida a zauren majalisar saboda rashin halartar wadanda za su jagoranci tattaunawar majalisar.
Kudirorin da majalisar ta dakatar sun kunshi gyaran babbar hanyar Bauchi/Gombe/ Yola, amfani da siminti wajen gina hanyoyi da dai sauransu.
Cikin ‘yan majalisar da basu halarci zaman majalisar ba sun hada da Ali Isa (PDP-Gombe), Obinna Chidoka (PDP-Anambra), Olemija Stephen (APC-Ondo) da Abbas Tajudeen (APC-Kaduna).
Daga karshe shugaban kwamitin kula da dokokin majalisar Orker Jev ya shawarci sauran ‘yan majalisar da su yi dunga sanar da sakatariyan majalisar idan ba za su sami zuwa zaman majalisar ba a lokacin da ya kamata domin hakan zai taimaka musu wajen ci gaba da gudanar da sauran harkokin da ke gaban su.
A cikin makoni uku da suka wuce majalisar wakilan ta dakatar da yin muhawara akan wasu kudirori saboda wadanda zasu jagoranci muhawarar basu halarci zaman majalisar ba.