ZAKI BIAM: Buhari ya jajenta wa mutanen jihar Benue

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajenta wa mutane da gwamnatin jihar Benue a dalilin harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwan Zaki Biam wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkar yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan.

Buhari ya ce harin da ‘yan ta’addan suka kai abin nuna juyayi ne akai sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi gaggawan gudanar da bincike akai sannan a hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Daga karshe Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan sannan ya shawarci mutanen kasa Najeriya da su zauna da juna lafiya.

Share.

game da Author