Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki yace ba bu hannunsa akan badakalar motar da hukumar kwastam ta kwace a dalilin rashin takardun gaskiya.
Wani mai taimakawa shugaban majalisar Yusuph Olaniyonu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya saka ma hannu inda ya ba da bayanai cewa ita motan kwastam ne ta kama a hannun wanda ya shigo da ita amma bai kai majalisa ba ballantana ace wai har Saraki ya karbi motar da za’a ce wai shine yake da mallakinta.
Majalisar dattijai ta mika wannan korafi da akeyi akan shugaban majalisar zuwa ga wata kwamiti nata domin ta binciki korafin sannan ta mika mata sakamakon binciken da tayi nan da makonni hudu masu zuwa.