Kotu ta bada umurnin a kama jikan Marigayi Ahmadu Bello, Magajin Garin Sokoto

2

Kotu a jihar Sokoto ta bada umurnin a kama jikan marigayi Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, Magajin Garin Sokoto, Alh. Hassan Danbaba.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan wata kara da Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa Maso Yamma Inuwa Abdulkadir ya shigar a gabanta ya na neman kotu da ta bi masa hakkinsa akan maganganun cin fuska da Magajin Garin Sokoto din yayi akansa.

Yace Magajin Garin Sokoto Hassan Danbaba ya yi masa kazafin cewa wai ubansa bawa ne wanda wata mata mai suna Goggo ta siya akan shilin biyu kudin mutanen da.

Lauyan wanda ya shigar da kara wato Inuwa Abdulkadir ya roki kotu da ta umurci Sifeto Janar din ‘yan sanda Idris Ibrahim da ya kamo Magajin Garin Sokoto a duk inda yake a kasannan.

Koda ya ke hakan bai samu amincewar alkali ba amma ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto da ya kama shi a duk inda ya boye a fadin kasarnan.

Duk da cewa Magajin Garin Sokoto ya bukaci kotu da ta dakata akan ci gaba da sauraron karar, alkalin bai amince da hakan ba.

An daga ci gaba da shari’ar zuwa 6 ga watan Afrilu.

Share.

game da Author