Shuagaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi dajin Sambisa ranar litini domin bude wasan gasar nuna kwarewa na sansanonin Sojin Najeriya da za ‘a fara ranar litini.
Janar David Ahmadau wanda shine shugaban shirya wasan yace an shirya wannan gasar ne a dajin Sambisa saboda a nuna wa mutane cewa an fa kwato dajin daga hannun kungiyar Boko Haram sannan sojin Najeriya din ta mai da dajin filin gudanar da gasar ayyukan soji na kasa daga yanzu.
Yace za’a kara ne tsakanin sansanonin sojoji dabam da bam inda sansanin da tayi fice za a bata kofi, mai suna kofin babban hafsan sojin Najeriya.
Za’a fara wasan ne daga ranar 27 zuwa 31 ga watan Maris.