Buhari ya nada sababbin shugabannin Bankin Manoma
Babban darekta a ma’aikatan aiyukan gona da raya karkara Blessing Lere-Adams ta sanar da sababbin nadin shugabannin Bankin Manoma na Kasa (Bank of Agriculture).
Wadanda shugabn kasa Muhammadu Buhari ya anmince da nadin na su sun hada da Kabiru Mohammed a matsayin shugaban Bankin.
Sauran sun hada da Prince Akenzua daga Kudu maso kudu, Okenwa Gabriel daga kudu maso gabas, Ameh Owoicho daga Arewa ta tsakiya da Bode Abikoye daga kudu maso yamma.
Blessing Lere-Adams ta ce shugaban kasa yayi hakanne domin ya dada samar da sauki ga manoman kasa Najeria.
Discussion about this post