An hana acaba, bara a titunan Kaduna daga yau

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hana Acaba da bara a tituna da manyan biranen jihar.

Gwamnati ta ce daga yau za’a kama duk wanda ya ke yin Acaba ko kuma aikata bara a manyan tinunan jihar.

Kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwan bayan taron kwamitin tsaron tsaron jihar da akayi a fadar gwamnatin jihar.

Sanarwan ta ce da ma can akwai dokar hana Acaba a jihar an dan daga kafa bne domin gwamnati ta gama wasu ayyuka da takeyi, amma daga yau an dakatar da hakan.

Share.

game da Author