Masarautar Bauchi ta dakatar da Wazirin Bauchi, Bello Kirfi

0

Masarautar Bauchi cikin jagoranci Sarki Rilwanu Suleiman Adamu ta sanar da dakatar da Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi.

Hakan ya na kunshe ne a wata takarda da jami’i mai kula da harkar yada labarai na masarautar Salmanu Yakubu Lame ne ya ba manema labarai a garin Bauchi.

Dakatarwan ta fara aiki ne nan take.

An dakatar da Waziri Kirfi ne saboda aika ta wadansu irin dabi’u da basu dace da masarautar ba a matsayinsa na Waziri.

Ko da yake ba’a fadi takamammen abinda yayi ba wata majiya ta ce dakatar wan zai yi nasaba ne da wata cecekuce da ya faru tsakanin sa da Alh Adamu Aliyu Walin Katagum bayan Sallar Juma’a a babban masallacin Bauchi wanda hakan bai yi wa Sarki Rilwanu dadi ba.

Share.

game da Author