Dalilin da yasa na shirya fim din ‘ABU HASSAN’ – Zaharaddeen Sani

1

Zaharadden Sani wanda ya shirya fim na farko da ya nuna dabi’u irin na ta’addancin da musamman irin wanda kasa Najeriya tayi fama dashi a dalilin ayyukan kungiyar Boko Haram ya fadi dalilin da ya sa ya shirya irin wannan fim din.

A hiran da ya yi da gidan jaridar PREMIUMTIMES ya ce ya shirya irin wannan fim dinne domin ya nuna wa duniya Illar da take cikin irin wadannan ayyuka da yadda iya’ye za su kula da ‘ya’yansu. Ya kuma ce fim din ta nuna yadda jami’an tsaro suma suke arangama da irin wadannan mutane da mabiyansu.

PT: Menene dalilin da ya sa ka yi fin akan aiyukkan ‘yan ta’ada?

Zaharadden: Ni dan Najeriya ne dake kishin kasa sannan ina so in nuna wa mutane irin illolin dake tattare da ayyukan ta’addanci da irin wahalhalon da wadanda akayi garkuwa dasu ke shiga.

PT: Mun sami labarin cewa ka dan sami takaddama akan samun amincewar hukumar tantance fina-finai ta ki amincewa da fim sannan sai da ka je hukumar SSS domin hakan?

Zaharadden: Da yake ba’a taba samu ko yin irin wannan fim din ba hakan ya za ma wani sabon abu a wajen masu bada takardan amincewa wa fina-finai kuma saboda bindigogi da kayayyakin da muka wanda yayi kama da na ‘yan tsagera shine yasa muka samu dan r hukumomin da hakkain hakan ya shafa.

A hukumar SSS sai da suka kalla sannan sukayi mini tambayoyi da da ama akai sannan suka bani shawarwari akan hakan.

PT: Me zaka ce akan matsalolin da ka fuskanta yayin da ka ke yin fim din?

Zaharadden: A gaskiya zuciya ta bata karaya ba domin wayar da kan mutane nake so in yi akan aiyukkan ‘yan ta’ada a fim din. Koda mutane suka tambaye ni akan rashin jin tsoron yin fim din na fada wa hukumar tantance fina-finan da kuma hukumar SSS cewa na yi fim din ne a matsayina na dan wasan kwaikwayo kawai.

PT: Menene fim din ya kunsa?

Zaharadden: Fim din akan wani dan ta’adda ne wanda yake yin garkuwa da ‘yan mata kuma ya bukaci sai an biya shi makudan kudi kafin ya saki matan. A wasu lokuttan ma bay a maida wa iyayen yaran ‘ya’aynsu ko bayan ya karbi kudaden.

PT: Menene ya baka karfin gwiwan yin wannan fim din?

Zaharadden: Na sami karfin gwiwan yin hakan ne saboda ira-iran fina-finan da na kala akan Sadam Hussein na Iraq, Gaddafi, Osama Bin Laden da sauran su.

PT: Yaushe fim din zai fito?

Zaharadden: Fim din zai fito a watan jibi domin mun kusa gamawa kuma zan turo muku fim din domin ku kalla.

Karanta hirar a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-X3L

Share.

game da Author