An fara saka wa shanu na’urar da za’a gano duk inda suke

0

A dalilin matsananci satan shanu da akeyi wanda yaki ci ya ki cinyewa an fara saka wa shanu wata na’urar da duk inda shanun suke za’a gano su.

A wata ‘ yar sanarwa akan hakan da Dr. Aliyu Tilde yayi a shafinsa na Facebook yace da zaran an kama shanu mai dauke da wannan na’ura za’ a san daga Inda suke.

“Karshen Satar Shanu Ya Zo

“Dazun nan Malaman shanu suka bar gidana bayan sun saka wa kowacce saniyata wani digon na’ura a cikin jiki wanda zai taimaka wajen gano duk inda take a duniya. Wannan ba karamin cigaba ba ne. Babba ne.

“Da N2,000 kacal za ka iya kare bijiminka da ya kai rabin miliyan na Naira. Ka ga idan barayin shanu suka gane za a gane saniya, ko ba za a yanka ta, ko a loda ta a mota, ko a sayar da ita sai an tabbatar da mai ita, dole su canza sana’a.

Daga karshe yayi kira da a sanar da makiyaya da manoma wannan gagarumin cigaba da aka samu.

Share.

game da Author