Kamar yadda a ka sani ne cewa a duk lokacin da yanayi ya canza zuwa lokacin zafi mutane musamman yara kanana su kan kamu da cutar Sankarau.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar da mutuwar mutane sama da 280 a dalilin kamuwa da cutar.
Akwai wasu alamomi da yake nuna cewa mutum ya kamu da cutar.
Wata babban likita mai suna Adefunke Babatola, da muka tattauna da ita akan ta bamu bayanai akan alamomin cutar tace “ Cutar yana kama mutane ne idan lokacin zafi ya zo.”
Alamomin su hada da:
1 Za ka ga yaro yana ta suma idan ya kamu da cutar.
2. Yawan kwanciya da gajiya
3. Yawan yin Amai
4. Cutar na kawo amai.
5. Curar na kawo zafin jiki wanda daga baya yakan iya zama Zazzabi.
6. Mutum zai dinga ganin jiri
7. Sankarewan wuya.
8. Rashin son ganin haske.