Cibiyar kula da bada kariya ga cututtuka ta kasa ta sanar da mutuwar mutane 282 sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau.
Shugaban cibiyan Chikwe Ihekweazu ya kara da cewa an gano wadansu dauke da cutar ss 1966 sanna kuma wasu su 109 sun sami sauki daga cutar.
Jihar zamfara ce ta ke da yawan wadanda suka rasu a dalilin cutar, Jihar Sokoto na bi mata sai Jihar Katsina da jihar Neja.
Ma’aikatar kiwon lafiya na babban birnin tarayya ta sanar da mutuwan wani mutum daya yau a dalilin kamuwa da cutar sankarau.
An sanar da rasuwar wasu guda hudu jiya a unguwan Durumi ta dalilin kamuwa da cutar.
Sakataren hukumar cibiyoyin lafiya na matakin farko Rilwanu Mohammed ya shawarci mutane da su daina yin cinkoso a wuri daya sannan a dinga bude taguna da kofofi domin samun isasshen iska.
Yace anyi wa yara sama da 17,000 rigakafin cutar dake garuruwan dake babban birnin tarayyan.