Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, Mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuf Lasun da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Ahmed Lawan sun tafi kasar Ingila domin gani wa kansa halin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake ciki.
Tawagar dai sun bar kasa Najeriya ne yau kamar yadda sanarwar hakan ta fito da ga bakin mai taimaka wa shugaban majalisar dattijai akan harkar watsa labarai Yusuph Olaniyonu yace.