Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, da Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal yau a Gidan Abuja dake birnin Landan.
Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, Mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuf Lasun da shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai Ahmed Lawan sun tafi kasar Ingila domin gani wa kansa halin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake ciki.
Tawagar dai sun bar kasa Najeriya ne yau.