Wasu kamfanonin masu zaman kansu za su wadata kauyuka 25 da wutan lantarki

0

Kamfanin ‘Community Energy Social Enterprises Limited, CESEL’ da ‘Renewvia Energy Corporation’ zasu wadata wasu Kauyuka 25 a fadin kasa Najeriya da wutan lantarki dake amfani da hasken rana wato Sola.

Jihohin da zasu fara amfana da wannan aiki sun hada da Jihohin Bayelsa, Ondo, Ogun da Osun.

Darektan kamfanin CESEL Patrick Tolani da darektan Renewvia Clay Taber ne suka wakilci kamfanonin su wajen sanya hannu a takardun yarjejeniyar a Abuja.

Ana sa ran za’a kashe sama da dala dubu 767 a aikin.

Sign

Tolani ya kara da cewa gwamnati za tayi hakanne domin samar wa wadannan garuruwa wutan lantarki kuma za su dunga biyan kudin wuta kamar yadda kowa yake biya bayan an gama aikin.

Tolani ya ce mutanen kauyukan da za’a samarwa wutan sola din ba za su yi fama da rashin wuta ba saboda hasken rana kawai na’urorin ke bukata suyi aiki.

“ Kudin wutan ma za su dunga biya ne ta wayar tafi da gidanka idan suka so.”

Daga karshe yace yace za’a gama aikin ne cikin shekara daya.

Karanta Labarin a shafin mu na turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-Wa2

Share.

game da Author